Lesson (2)
Week 2
(The Process of Web Design) Hanyoyin da zamubi kafun ace
munfara tsara shafinmu na yanar gizo,
Mafi akasarin mutane suna samun matsalane awajen kirkiran yanar gizo,
akwai hanyoyin da yadace ace anbi, kafun afara kirkiran yanar gizo, saboda
agujewa matsalolin, dazasu faru ciki, kokuma idan mtsala tafaru asamu
hanyan tarota, dan duk abunda akayishi akan tsari to yanada saukin gyara
koda ace yabaci, so ga jerin hanyoyin daza’abi kamar haka.
1. Nafarko Ance (planning) Ma’anarsa tsarawa,
Amatsayinka na mai Tsara Yanar gizo, kafun ace kafara tsara yadda kakeso ya
kasance, yakamata katambayi kanka wannan tambayoyi, sannan kabawa kanka
ansarsu, nafarko,
Menene burina akan wannan rukuni na yanar gizo dazan kirkira?
Suwayene wadda zasuna ziyartar wannan rukunin nawa na yanar gizo?
Menakeso masu ziyartar suyi acikin shafin nawa na yanar gizo?
So atakaice idan kasan wannan abubuwan to kataka matakin farko akan yadda
tsarinka zaika sance.
2. Nabiyu shine (content building) ma’anarshi shine yadda cikin shafin zai
kasance, idan anginashi.
Zaka gina duk abunda kakeso bayan duk wani tsare tsarenka yakare, daganan
zakafara, gina shafin naka, sannan abuda yakesawa shafinka yasanu, shine
kamar yadda nafadamuku, aginashi akan tsari, dakuma akan abunda mutane
sukafiso, shine ma’anar tambayoyin da kayiwa kanka,
Kuma aduk lokacin da mutane suke yawan shiga shafinka, zaka samu kudi,
sannan zaka samu lada, idan kasa abunda mutane zasu karu dashi, tareda
matsayi mafi girma agurin (google),
Sannan akwai shawarin da zan bayar akai.
Misali idan burinka kaginane saboda kadaura takardun karatu, ko kasaida
kayan lantarki wato (eletronics) ko wajen sauraren wa’azi, ko wajen sauraren
wani rukuni na fannin binceken likitanci, ko makamantan haka,
Sai kayi nazari awane guri kake rayuwa, wa enne irin mutanene, suke rayuwa
agurin, kuma mesukeso,
Sannan kafara tunanin mexakayi, bawai idan abu yaburgekaba kace zakayi
ba kadubi abunda al’ummar wajen sukeso, tunda shi shafin yanar gizo dan alumma akeyinshi, inaga zaifi dacewa. Allah yasa ayi asa’a bijahee annabi
(saw).
Misali bari nabaku yadda tsarin zaikasance kamar haka
Kamar yadda kukaga wannan photon asama, munada inda aka rubuta (Homepage) to shiwannan shafin an hadashine da duk shafukan dasukeci, idan kun lura zakuga layukan dasuka hadasu, shafi bayan shafi,
Wato shi home-page an hadashi da shafuka guda hudu, kamar yadda kuke gani, sannan daga cikinsu, shafuka guda biyu, an hadasu da sauran shafuka, daga ciki akwai shafin wakoki, idan kashiga homepage sai kaje music, sannan daga cikin music ma akwai shafuka, kamar yadda kuka gani, akwaisu country, da hip hop, da classical, da rock, wanna duk shafuka wanda suke karshin shafin, music wato waka. duk wanda kashiga zakaga wakoki aciki.
Atakaice wannan shi ake kira (Hyperlink) ma’ana ka kirkiri shafi ka hadashi da wani. Wani cikin wani.
Allah yakara mana fahimta bijahee annabi (saw).
1. Masu zane wato (Design),
Kamar yadda kukaga anzana waccen nasaman shafi bayan shafi, to mafi akasarin masu zane na yanar giro suna samun matsalane, daga, lokacin zanen shafi, misali sai kamanta ka tsallake shafin farko ko na biyu,
To su wannan masu zanen shafin yanar gizo ana cemusu (system analyst)
Sai an kaimusu sun zana kafun akawowa mai kirkira da yaren kwamfuta wato programmer sannan yayi amfani da language na html, wato yaren da kwamfuta takeji sannan yabi zanensu kamar yadda aka yatsara,
Misali shi mai zane wato (system analyst) shine kamar engr. Shikuma programmer shine magini,
Kunsan idan za’ayi gina wata babbar makaranta sai ankira Engineer, yazo yazana plan din wato filin Kenan, sanna mai gini yazoda kayan aikisa, yabi zanen da engr. Yazana masa, yayi aikinsa,
To idan shi engr. Yayi kuskure wajen zane kunga ay dole magini yayi kuskure, wajen yin gini.
Babban abunda nakeso kugane anan shine, duk wani babban shafin yanar gizo mutun daya bayayi shikadai, sai ansamu ma aikata kamar yadda najero muku kowa yayi aikinsa,
Idan kuma karamar shafice aka kawoma kamar, dan wani ma’ajiyar takardu ko wakoki ko videos da makamantansu, zaka iyayi kaikadai, duk wanna ayyukan kaika dai zakayisu, saboda babu wani tsare tsare dayawa, acikin Abunda za’ayi bazaifi karfin kaba.
Kamar yanzu zaka gina gida mai daki biyu ko uku, ay ba sai kakira Engr ba kai da kanka zaka tsara kayanka. Inafata amfahimta,
Allah yakaraman kaifin basira bijahee annabi (saw).
Comments
Post a Comment