Python Lesson 2
Week 2 Python syntax:
Python syntax ana gudanar dashine directly a command line ko kuma a kirkiri python file akan
server wajen amfani da .py extention sannan kuma ayi running dishi akan command line
Python identation: a wasu programming languages din indentation ana amfani dashine wajen
saukin karanta layukan code amma a python indentation yanada matukar muhimmanci, python
yana amfani da indentation wajen bayyana block of codes
Misali:
if 5 > 2:
print("biyar tafi girman biyu!")
wannan space din kafin in rubuta print function shi ake kirada indentation
take python interpreter zata maida maka da error idan kacire indentation wajen block of codes
misali:
if 5 > 2:
print("biyar tafi girman biyu!")
kunga anan nacire indetation to hakan error zai bayar domin shi indentation yana tafiyane tareda
statement da aka bayar (if 5 > 2:)
COMMENT (DAN GAJEREN SHARHI)
Me'ake nufi da comment a Python bama Python kadaiba harda sauran wasu programming
languages din.
shidai "comment" wani dan Gajeren Sharhi ne da programmers suke amfani dashi yayin dasuke
rubuta program...
atakaice dai comment dan gajeren Sharhi ne wajen saukake ma sauran programmers fahimtar
line's na codes idan ana bukatar sabuntashi koda programmer din daya rubuta wannan program
din ya mutu ko baya nan
to comment yana bada dama mawasu sauran programmers fahimtar code koda
basu suka rubuta program dinba ko application din wajen sake ingantashi....(updating)
Sanna shi comment a yaren Python ana rubutashi ne ta hanya guda biyu akwai
1) Single line comment (wato gajeren sharhi na layi daya )
2) dakuma multiple line comment (gajeren Sharhi na layi sama da daya)
Misali
Sune kamar haka
#Arewa computer library
Misalin single line comment kenan bai zarce layi guda ba
Kuma ana fara rubutashi da alamar hash "#" symbol
Compiler/ dakuma interpreter idan sukaga wannan rubutun take zasu dauke shi
matsayin gajeren Sharhi
misali na multi line comment wato gajeren sharhi sama da layi daya
Shi ana fara shine da alamar quotation mark har guda uku
""" Arewa computer library saita
shiga jahohin arewa lungu da sako insha Allah namba da dadewaba"""
python comment ana amafani dashine wajen documenting na codes Dinka domin fahimatarsa ga
sauran programmers idan amfanin hakan yatasu
misali:
#This is a comment.
print("Arewa computer library!")
DOCSTRING:
Shima docstring comment ne na wanda yak ama daga layi daya zuwa layi biyu ko sama da haka
Misali:
"""wannan shine
multiline docstring."""
print("Hello, World!")
Wato comment sama da layi daya zuwa biyu.
Comments
Post a Comment