Python Programming (1)

 



AREWA COMPUTER LIBRARY

COURSE: PYTHON PROGRAMMING 1

INSTRUCTOR: DAWUD ABUBAKAR

Week 1

INTRODUCTION:

MENENE COMPUTER PROGRAMMING LANGUAGE?

Computer programming language) wani Yarene wanda kwamfutoci ke iya

fahimtarshi kuma yana tafiya ne bisa doran wasu tsare tsare da dokoki ( kamar dai yarukan 

damuke yi na yauda kunlum )

MENENE PYTHON PROGRAMMING?

Takaitaccen Bayani Akan Yaren Python Programming!

Python sanannen yaren na'urane (programming language) python yashiga

wurare daban daban wajen gudanar da ayyuka ma banbanta na kowani fanni sabida saukinsa 

dakuma dadin aiki wajen sarrafa yaren 

python yarene na manya-manyan matakai (high-level language) misali kamarsu C, C++,

java, PHP etc.

Wanda ya kirkiri Yaren python shine Guido van Rossum, wanda ya fitar dashi duniya a

shekarar 1991. sannan akacigaba da ginata da ingantata karkashin (Python software

foundation).

Python yare ne mai sauƙi wanda ke da sauƙin koyo...

Python na iya yin aiki a dandamali daban-daban (operating system ) kamar su Windows, Mac,

Linux, Rasberi Pi, da sauransu. Yana gudana ne a kan tsarin fassara

(interpreter) wannan yana nufin za a iya aiwatar da codes dinsa cikin sauki da

zarar an rubuta Python yare ne mai saurin aiki domin yanada gajerun layukan codes.

Python ya fi sauƙin tsare tsaren wajen rubuta program akan wasu harshen kwamfuta damuke dasu 

Akwai banbance banbance tsakanin python versions wanda yakama daga kan

Python. 2 dakuma python 3 wajen tsarin rubutun codes dinsu...Dangane da

wannan ajin namu zamuke anfani da python.3 ganin cewa shine yanzu kusan

kowa da wannan version yake aiki. Abu nagaba inason kowa na wanna aji namu yasami kayan 

aiki ma'ana python IDE wajen rubuta python programs dimnu sune kamar haka

1) wadanda suke da android kadai zasu iya downloading din wannan

manhajar a playstore kawai kushiga wajen bincike kurubuta

Pydroid 3 Ko kuma Qpython3L

Note: Zaku iya downloading dukkansu biyun inaga Zaifimana sauki domin suna aiki aiki ko 

babu

data akwai dayawa wasu IDE din saida data suke amfani wajen gudanar da aikinsu

2) Ga wanda zasuyi amfani da kwamfuta kuma zasu iya neman manhajar IDE na python cikin 

kwamfutarsu sune kamar haka...

1) www.python.org

2) Pycharm IDE

2) Thonny IDE

WASU KALAN AIKI AKEYI DA YAREN PYTHON?

1) Web development (server-side)

2) Web applications

3) Software development

4) Mathematics computational 

5) System scripting

6) Game development

7) Artificial intelligence (AI)

8) GUI Desktop app

9) Data analysis ETC

KADAN DAGA CIKIN AYYUKAN YAREN PYTHON

(programming language).

Sannan yana bama programmers dama surubuta codes cikin kankanin layi..

1) Web Development abinda ake kira da web development shine ginin yanar gizo, ko ƙirƙirar 

yanar gizo dakuma kula dashi kanshi yanar gizon shi web development ya konshi frontend duk 

abinda ya shafi client dakuma backend sannan dakuma kulla alaka da Databases ( matattarin 

bayanai Ko ince runbun bayanai )

2) Web application kwamfuta program ne wanda yake amfani da browser yanar gizo domin yin 

wani aiki ko kuma bincike kan yanar gizo

2) Web applications client sever program ne ma'ana anan shine yanada client side

dakuma server side.

Misalin web apps

Shopping cart, online forms, word processor.. etc

3) Software development wani fagene dake ba computer programmers wajen gina ko ƙirƙirar 

manhajar computer cikin wasu tsare tsare da dokoki dake ba kwamfuta Damar aiki cikin sauki.

4) Mathematical computational ana amfani da Python wajen lissafi mai tsaurin gaske wajen 

warware wata matsala cikin sauki dakuma samun abinda ake nema batare da wahala ba fiye da 

wasu Yaren.

5) System scripting. Ko kuma System script wani Yaren kwamfuta ne na musamman wajen bada 

umarni ga programs kamar (web sites ) wanda kwamfuta ke amfani dasu wajen binciken yanar 

gizo

Misali markup languages kamar HTMl, css etc

6) Game development ana amfani. Da Python wajen cigaban kirkiran ko gina kwamfuta game 

sabida saukinsa wajen bada Umarni Python yana daga cikin Yaren da yawancin kwamfuta games 

ankirkire sune da python..

Misali kamar game din da yawancin kowa yasanshi

.......Snake game......

7) Artificial intelligence: Artificial intelligence python shine kusan Yaren da ake amfani dashi 

wajen

programming na kwamfutoci masu fikira da hangen nesa (sakago wato robot) wajen basu 

umarni domin gudanar da ayyukanshi batare dawata matsala ba...

8) Data analysis python shike taka rawar gani da ganin cewa an gudanar da

lissafin tarin gundarin jawabai cikin sauki....Shi ake kira da Data science..

Da sauransu ...........

MANYA MAYAN KANFANONI DASUKA SHAHARA ADUNIYA

WANDA SUMA SUNA AMFANI DA PYTHON

Kuma suna gudanar da wasu ayyukansu da Yaren python sune kamar haka:

1) Facebook

2) Google

3) Instagram

4) Spotify

5) Quora

6) Netflix

7) Dropbox

8) Reddit

9) Uber

Da sauransu.....

Wadannan manyan kanfanonine da kusan anan kowa yasansu kuma dukkansu wasu anginasune 

da Yaren python wasu kuma sun hada da Python wajen ƙirƙirar manhajar su da kayatashi, Kusan 

acikin wadannan kamfanoni kamar

1) instagram da kuma

2) Dropbox

3) Pinterest

4) Uber kusan kaso 80 cikin 100 anyi sune da Yaren python... kuma dukkansu da Yaren python 

aka kirkiresu...

Comments