Web Design Lesson (1)
WEB DESIGNWeek 1(INTERNET) WAI SHIN MENENE INTERNET.Intanet wasu jerin hanyoyin sadarwar ne na kwamfuta da sauran na’urori dake dahaɗin kai a duniya, wadda jama'a suke samun damar watsa baya nansu ta hanyar binka idoji da aka tanadar musu, wadda hukumar (Internet Assigned Numbers Authority(IANA) ta tanadar,
intanet na nufin tsarin sadarwa na duniya, da suka hada da na'urorin hannu da ababenmore rayuwa, yayin da yanar gizo ke daya daga cikin ayyukan da ake yadawa tahanyar intanet, inda mutane suke samun dama su kirkiri shafin yanar gizo, akaninternet, domin su adana baya nansu, ko kuma su tallata ra a yoyinsu, na kasuwanci,kamar yadda kamafanonin sukeyi irinsu (amazon) da (jiji) da dai sauransu,so wannan duka shafine na yanar gizo, insha allah zamu kawo muku bayanai akanyadda ake kirkiran shafi akan yanar gizo na duniya wato (www).
SHIN MENENE (WWW).
Mafi akasarin mutane, wasu sunsan meye “www” yake nufi wasu kuma basu saniba,
to ga bayani kadan daga ciki,
WWW yana nufin yanar gizon na duniya, A turance ana cemasa world wide web
(www) misali,
Gidan Yanar Gizo na Duniya ana kiransa Web
Yanar Gizo cibiyar sadarwa ce ta kwamfutoci da sauran na u’rori a duk faɗin
duniya
Duk kwamfutocin dasuke cikin gidan yanar gizon suna iya sadarwa a tsakaninsu,
Sannan dukkanin kwamfutoci suna amfani da tsarin sadarwa mai suna
HTTP
TAYA (www) YAKE AIKI.
Na daya ana adana bayanan yanar gizo a cikin takaddun da ake kira Shafukan
Yanar Gizo,
Na biyu ana adana wasu bayanai masu muhimmanci kamar irin bayanai na
ma aikatan kamany, kokuma bayanai na ko wane mutum, akan kwamfutotin
da ake kiransu (web server).
Na uku kwamfutotin da ake karanta shafin yanar gizo dasu Sukuma ana
kiransu da (web clients).
AWANI BANGARE KUMA SHI (www),
Ana aiki mai kayatarwa dashi, akan internet, bisa fasahar da ake kira Hypermedia,
idan ance hypermedia bawai yana nufin bayanai na rubutu kadaiba, yahada da,
fotuna, bidiyo, da kuma rubutun, zaka iya hada bayanai shafi bayan shafi, kuma
kadorasu akan internet, bisa dokar da’aka tanadar, har jama’ar duniya susamu su
ziyarci wannan shafin nakan, game da abunda kake dorawa, ko yashafi kasuwanci
ko kuma ilimantarwa, allah yakaraman hasken ilimi bijahee annabi (saw).
ME AKE NUFI DA “WEBSITE”
Shi website wani gidane wadda ake tara shafukan yanar gizo aciki, kamar takardun
karatu, wanda dalibai suke iya ziyarta, ko kuma shafin bidiyo, fotuna, wakoki, ko
kuma graphics inda mutum zaije ya kalla ko yayi downloading ko sayan wani abu
da ya burgeshi aciki,
Misali kamar kaziyarci. Wani gidan yanar gizo, ko kuma wani abokinka yakawoma
shawari, yacema akwai wata makaranta datake koyarda ilim fasaha da yarenmu na
hausa a arewacinmu na Nigeria, ko kanada labarinta, anacemata (arewa computer
library),
Sai ya baka adireshinta na yanar gizo misali saikace ya hau internet yaje matattaran
bayanai, wato (browser) ya rubuta www,arewacomputerlibrary.com zaiga abun
mamaki game dasu.
To abunda nakeso ku fahimta game dasushine, wannan shafin da kuka ziyarta inda
zakuje kuga bayanai, da fotuna da bidyo dadai sauran abubuwan dabaza a rasaba,
kashiga wannan shafin kafuta kashiga wani, shi ake kira da (website) adunkule, inda
aka tara shafuka waje daya, misali shafin, littatafai, da bidiyo dana waka an hadasu
guri kuda.
Kamar kamfanin www.amazon.com da www.jiji.com dukansu za’a kirasu web site,
saboda sun kunshi shafuka dayawa acikinsu. Allah yakara fahimta bijahee annabi
(saw).

Comments
Post a Comment