Computer Fundamental Darasi Na 3
Day 3. Topic: 3
Topic: System Unit
Yau zamu tattauna akan Topic din: System Unit.
Wato Rukunin tsare-tsare kenan, shima wannan yana dauke da duk lamarin da ke dauke da dukkan kayan aikin lantarki (Electronic Components) na kowace irin kwamfuta.
"Electronic Components" suna ɗauke da "Internal Hardware" ganin cewa suna cikin sashin tsari wato system unit kuma ba zaka iya ganinsu ba koda kuwa ka kalli kwamfutar.
Waɗannan abubuwan da aka haɗa a cikin (System Unit) wato naúrar tsare-tsare, sune suke aiwatar da bayanai kuma da gaske suke sanya kwamfutar aiki.
"Internal Components" din sune kamar haka:
1. Power Supply: Power supply yana canza wutar lantarki zuwa ayyukan da ake cikin tsaka da yi a cikin kwamfuta. Lokacin da kwamfutar ke kunne power supply tana bada damar sauya wutar lantarki zuwa wasu abubuwan da ke cikin kwamfutar.
2. Motherboard: Motherboard itace "Circuit Board" wacce take da iko da mafi yawan "Internal Components" na kwamfuta A motherboard akwai manyan katuna guda uku; katin sauti (Sound Card) wanda ke aiki da sauti, katin bidiyo (Video Card) wanda ke ɗaukar hoton da kuke gani akan monitor da kuma modem card wanda ke bawa kwamfutoci damar sadarwa da juna. Har ila yau, a jikin Motherboard akwai "Central Processing Unit (CPU), processor ko kace kwakwalwar kwamfutar ma gabadaya (CPU) yana sarrafa bayanai kuma yana gaya wa sauran abubuwan da ke cikin kwamfutar abin da za su yi.
RAM & ROM: RAM yana nufin "Random Access Memory". Wannan memory din yana riƙe da bayanan da kuke aiki yayin da kwamfutar ke kunne. Da zarar ka kashe kwamfutar duk bayanan da suke cikin RAM zasu tafi. Shi kuma "ROM" yana nufin "Read Only Memory" shi kuma Wannan Memory yana dauke da bayanan da zaka iya karanta su, amma ba za'a share su ba. Bayanan dake a cikin ROM an gina su kuma koyaushe suna nan koda lokacin da kwamfutar ke kashe.
Comments
Post a Comment