Computer Fundamental Darasi Na 5

 Topic: Gyara da kanikancin kwamfuta.


Wato duba da wannan lokaci da muke ciki a yanzu, an samu wayewar Kai sosai especially a harkar na’ura  mai kwakwalwa.


Kamar yadda kukasani a yanzu kowane ma’aikaci na office ko asibiti, ko gona ko magidanci ne ko dalibi ne, ko dan kasuwa, kowanne daga cikinsu kokarinsa ya iya kwamfuta duba da cewa ita computer tana da sauri gurin gudanar da aiyuka a saukake. Hakan yasa masu amfani da ita suka yawaita..


Kamar yadda nake fada dai ita computer abuce mai bukatar kulawa akai-akai, wasu zakaga duk bayan lokaci zuwa lokaci sukan kai na’urorin su gurin maintainance kamar ma’aikatan Banki da makamantansu.


Shi wannan maintainance din bakomai bane illa duba lafiyar computer ko na hardware ko na software domin gujewa matsaloli irin nata...


Hanyoyin da zakabi domin warware matsalolin kwamfutar ka..


Duk lokacin da ka lura da kwamfuta dinka ta samu matsala, idan har ba matsalar lalacewar wani component bane daga cikin kwamfutar ba, to tabbas ba buqatar ka kaiwa mai gyara kabiya shi 2k ko sama da haka ga matakan da zaka bi domin gano matsalar na'urarka..


1. Abu na farko da zakayi shine kayi restarting na kwamfuta din taka, Idan har kayi zakaga "pop up" din matsalar Ya sake bayyana a screen din kwamfutar.


2. Abu na biyu ka tabbatar da duka programs dinka dake ciki da drivers sun zama up to date, wato kayi Updating dinsu kenan.


3. Sannan na uku ka tabbatar da antivirus software dinka yana aiki da kyau, Domin kuwa Kar hackers su samu dama, Ya kasance sune suka rikita maka na'ura, sannan ka yi kokarin gano me yake kawo irin wannan matsalar, meye dalilin da yasa takeyin irin wannan dabi’ar, sannan kuma shin problem din yana bukatar sai an bude system din kokuwa za’a iya shawo kanshi ba tare da an bude system din ba, kuma sau tari irin wannan case din software problem ne.

[5/10, 4:43 PM] Oga Saheel: Bari mu fara da matsalar da ta cika damun kwamfutocin mu a irin wannan lokacin.


Wato "PC-Overheating": idan har kwamfuta dinka ta cika yin zafi da yawa, a duk sanda ka kunna saikaji tana zafi sosai, Wannan zafin yana sa kwamfuta dinka tana yin slow sosai, wani lokaci ma har ya ja ta dinga daukewa kana tsakiyar aiki, Wani lokacin kuma sai dai kaji tana kauri saboda wasu abubuwan daga cikin ta su lallace sabida tsabar zafin da takeyi.

[5/10, 4:45 PM] Oga Saheel: Dole akwai Dalilin da yake saka ta take Overheating, na farko kodai cooling system dinka baya aiki yanda yakamata, gashi computar naka tayi zafin da cooling system din baya iya dauka ko kuma fankar system din bata aiki.

Me ya kawo Zafin ma tukun?, yanada kyau kasan dalilin da yasa computar take zafi, a duk lokacin da abu biyu ko fiye da haka suke aiki a cikin engine dole a samu zafi, a wannan yanayin GPU dinka ne da CPU suke aiki, iya yawan aikin su iya zafin da system takeyi.


Shine dalilin da yasa kake ganin kowane kwamfuta tanada fanka domin ta dinga sa iska yana yawatawa a ciki. Idan kana bukatar kaga iya zafin da system dinka take generating, se kayi downloading din 


HWMonitor app, zai taimaka maka wurin fahimtar adadin zafin da take dauka.


To Yanzu idan kwamfutar mu ta fada a wannan matsalar ya zamuyi mu warware ta..?


Farko zaka duba idan fankan ka tana aiki, ya za’ayi kagane tana aiki?, da ka kunna system din sai ka saurara, aciki zakaji tashin fankar idan ka kai kunnen ka kusa, in kuma bakaji ba, sai ka nemo screw driver ka bude kwamfuta din ahankali domin gani da idonka.



Abu na biyu ka guji blocking din mashigar iska na system din, ma’ana idan da abunda kaga ya toshe gurin shigar iskar, sai kayi kokari ka jaye abun, ka tabbatar da ka kakkabe kurar da kagani a cikin system din musamman wurin fanka din, domin kura ma tana daga cikin abunda ke saka system Overheating, daganan sai kayi amfani da blower ka hure kurar. Idan kuma zafin yaci gaba, kuma dai fanka na aiki yanda yakamata, ba Qura a ciki, Kawai Sai kayi downloading din manhajar "SpeedFan"

Zata baka damar ganin yanayin gudun Fankan sannan ka rage yin aiyuka da yawa da ita kamar yin kallo, yin game, downloading a lokaci daya.
Ina fatan kuna fahimtar matsalolin da hanyar warware su koh? 
Zaku iya cin abinci da wannan kananun matsalolin da kuke gani, idan kuka maida hankali
Ina fatan kuna fahimtar matsalolin da hanyar warware su koh? 
Zaku iya cin abinci da wannan kananun matsalolin da kuke gani, idan kuka maida hankali.

Comments

Popular posts from this blog

Graphic Design Lesson 2