Computer Fundamental Darasi Na 2
Day 2, Topic 2: Na'urorin Input (Input device):
Wato Na'urar shigar da bayanai ita ce duk wani kayan aikin (hardware) da zai baka damar amfani da bayanai ko shigar da bayanai a cikin kwamfuta.
Akwai na'urorin shigarwa da yawa. Shidda daga cikin wadanda aka fi amfani dasu sune kamar haka:
1.(Keybord) Maballin rubutu - Kuna amfani da maballin don buga haruffa, lambobi, da alamu a cikin kwamfuta.
2. (Mouse) --na'ura ce mai nuna alama wacce ke da alama a cikin computer wannan yana canzawa zuwa siffofi daban-daban yayin amfani da (Mouse) shi linzamin kwamfuta ne.
Kuna danna linzamin kwamfutar (Mouse) da sakin maɓallin madannin. Wannan aikin yana baka damar shigar da bayanai yayin amfani da linzamin kwamfuta (Mouse).
3. A Scanner - Wannan itace na'urar shigar da bayanai daga takarda zuwa kwamfutarka.
4. (Microphone) Makirufo - Ana amfani da makirufo galibi don shigar da murya a cikin kwamfuta.
5. (Digital Camera) - Kyamarar dijital tana baka damar ɗaukar hotunan da zaka iya shigar dasu cikin kwamfutarka
6. (A PC Video Camera) wato Kyamarar Bidiyo ta PC - Kyamarar bidiyo ta PC tana baka damar ɗaukar bidiyo
har da hotunan da zaka iya shigar dasu akan kwamfutarka.
(Output Device) wato Na'urorin fitarwa, Na'urar fitarwa ita ce kowane (Hardware) wanda ke ba da bayani ga mai amfani da kwamfutar.
Na'urorin fitarwa guda uku da ake yawan amfani dasu sune kamar haka:
1. A Monitor - Wannan na'urar fitarwa tana nuna bayananka ne akan allo, (Screen).
2. Printer - na'urar fitarwa ce da take buga bayanai akan takarda.
Wannan nau'in takardar (Printed Ouput) ana kiranshi da "Hard Copy".
3. Speaker - Sauti shine nau'in fitarwa da zaka samu daga Speaker.
Sauran manyan kayan aikin komputa da muke buƙatar bayani akai shine sashin tsare-tsare wato (System Unit)
Comments
Post a Comment