Graphic Design Lesson (1)
Graphic design ya samo asali ne tun daga farko wajen fara amfani da launi (color) kamar yadda tarihi ya nuna akan 'kasar Egypt, Mutanen nahiyar a lokacin suna amfani da launi (color) wajen yin zane-zanensu a cikin kogunansu na manyan duwatsu, domin suyi alama ta wani abu da suke so suyi nuni ma wani ko wasu dashi, ko zane na tambarin 'kungiyoyin jarumai, ko zanezane na makamai ko ma dabboni ( wannan yana daya daga manyan-manyan hanyoyin sadarwa na gani da aka fara samu a duniya)
An fara yin graphic design ne tun a shekarar 1920s inda aka fara zana sifa (shapes), tambari (logo), rubutu na zane (typography), da kuma ilimin zube na launi (color theory).
WILLIAM A. DWIGGINS ( THE FIRST GRAPHIC DESIGNER)
William Addison Dwiggins kenan wanda tarihi ke nuna cewa shine farkon graphic designer da duniya ta sani kuma ta yadda da cewa shine graphic designer na farko.
Ba'amurke ne, An haifeshi ranar 19 June 1880, a Martinsville, Ohio, United States. Ya mutu a ranar 25 December 1956, a garin Massachusetts da yake a United States, yayi shekarar 76 a rayuwarshi baki 'daya.
Idan mukabi tarihin graphic design tun a shekarun farko zamu ga cewa ya fara ne tun a farkon samar da rubutu da aka farayi, idan muka dauki hakan ba zamu ce William Addison Dwiggins bane graphic designer na farko ba, amma kasantuwar sauran mutanen na bayanshi basu dauki aikin da sukayi ba a matsayin graphic design kuma ba'ama samar da wani suna na graphic design ba a lokacin.
William Addison Dwiggins ya shahara wajen iya jera zane na rubutu tare 'kwalliyar haruffa (type designer & calligrapher) shine ma mutun na farko daya shahara a wannan fannin, kuma mai zane ne na littafi (book designer) ya kawo sauyi da cigaba sosai a bangaren kasuwancin litattafai wajen yin zane-zane masu daukar hankali da yin Bayani kan abunda littafi ya 'kunsa, da sauran wasu zane-zane da akeyi a cikin littafi.
William Addison Dwiggins yayi zane-zane na litattafai da dama, zan saka hotunan wasu daga cikin sanannun zanenshi a comment section.
Daga cikin maganganun William Addison Dwiggins yana cewa:
Whatever man loves, that is his god. For he carries it in his heart; he goes about with it night and day; he sleeps and wakes with it, be it what it may - wealth or self, pleasure or renown.
Ma'ana: Duk abin da mutum yake so, shi ne Allahnsa. Domin yana ɗauke da ita a cikin zuciyarsa; yana tafiya da ita dare da yini; ya kwana ya tashi da ita, ko ta yaya - dukiya ko kai, jin dadi ko shahara.
Martin Luther ne ya ruwaito wannan maganar.
✍🏼 Abu Ibrahim
Wannan shine William Addison Dwiggins
Paul Rand kenan 'daya daga cikin sanannun graphic designers na duniya. An haifeshi a Brooklyn, New York, United States. A shekarar 1914 ya mutu a shekarar 1996, yayi shekararshi 82 a duniya. Ya mutu ne a garin Norwalk Connecticut, dake United States, a ranar 26, November 1996, a sakamakon cutar cancer.
Bashi bane wanda ya fara yin graphic design a duniya ba, amma ana kiranshi da Father of Graphic Design saboda irin gudunmuwar daya bayar a cikin ilimin graphic design din, da kuma kwarewarshi a fannin graphic design.
Ya kasance malami a jami'ar Yale University (School of Art) dake New haven, Connecticut, United States. Ya shahara matu'ka a wajen 'kir'kirar logo da zane-zane na illustrations.
Shine wanda ya 'kir'kiri log na:
Enron, NeXt, ABC, da IBM
Zan saka hotunansu a comment section.
Basu bane ka'dai ba amma suna cikin sanannu daga cikin logos 'dinda shine yayi su.
A shekarar 1947 Paul Rand ya wallafa wani littafinshi mai suna "Thoughts on Design" wanda ya 'kunshi ilimin graphic design daya shafi fanni-fanni a cikin graphic design.
Wasu daga cikin masana ilimin graphic design na duniya suna cewa "ilimin graphic design ya samu 'karin daraja da kuma yin sau'ki wajen fahimta ma mutane ne daga lokacin da Paul Rand ya wallafa littafinshi na Thoughts on design"
Daga cikin maganganun Paul Rand yana cewa:
Don't try to be original; just try to be good.
Ma'ana: Kada ku yi 'ko'karin zama na asali; kawai kuyi kokarin zama nagari.
✍🏼Abu Ibrahim
Wannan shine Paul Rand
Graphic Design ƙirƙirace tafasaha ko muce sana'ar sadarwa ta
gani wacce take haɗa hotuna, kalmomi, da ra'ayoyi domin isar
dabayanai ga masu sauraro, musamman don samarda
takamaiman sakamako.
A wasu bayanan kuma graphic
design shine tsarin sadarwa, Hanya ce ta isardara'ayoyi
ta hanyar gani dazane.
Graphic Design ƙirƙirace ta fasaha ko sana'ar sadarwa ta gani wacce ke haɗa hotuna, kalmomi, da ra'ayoyi don isar da bayanai ga masu sauraro, musamman don samar da takamaiman sakamako.
A wasu bayanan kuma graphic design shine tsarin sadarwa, Hanya ce ta isar da ra'ayoyi ta hanyar gani da zane.
Graphic design aikine kuma darasi ne mai zaman kanshi wanda yake ba duk wanda ya iyashi damar samun aiki a ƙarƙashin wata masana'anta ko kuma dan ƙwadago mai zaman kanshi.
Abun da kowa yayi imani dashi shine graphic design ba ra'ayi bane ko aiki na baƙar fata da farin fata ba. Domin fahimtar ma'anar graphic design yana da muhimmanci a sami cikakkiyar fahimta game da duk wani abu da graphic design ya ƙunsa da kuma ƙa'idojin da suke aciki.
Kasuwanci
Siyasa
Waƙoƙi
Labarai
Finafinai
Bukukuwa
Wasanni
Wallafa littafi
Bikin Suna
Murnar gama karatu
Shagalin Sallah
Murnar Zagayowar Shekara
da sauraransu
Duk abunda za'ayi daga nan 👆🏼👆🏼 ciki ana buqatar graphic designer ya shigo ciki.
Elements of Graphic Design
Abubuwan da suke hada graphic design wato element kenan
Bangarorin ababen da suke haduwa su samar da graphic design tare da isar da saƙonnin da ake da buƙatar a isar na gani
Sune.....
🔰Line
🔰shape
🔰color
🔰typography
🔰texture
🔰size
🔰space
🔰 Line
Yana daga cikin abubuwa mafi muhimmanci masu samar da design.
Lines zasu iya zama masu lankwasa ko madaidaita, masu kauri ko kuma sirara, zasu iya zama masu baki biyu ko sama da haka.
Yana daga cikin abubuwa mafi muhimmanci masu samar da design.
Lines zasu iya zama masu lankwasa ko madaidaita, masu kauri ko kuma sirara, zasu iya zama masu baki biyu ko sama da haka.
🔰 Shape
Siffa wani yanki ne mai fasali wanda yake da girman gaske da aka kirkira ta layi. Nau'ikan siffofi daban-daban sun haɗa da siffofin geometric, abstract, da kuma siffofin halitta, duk waɗannan mahimman abubuwa ne da suke samar da design.
Siffa wani yanki ne mai fasali wanda yake da girman gaske da aka kirkira ta layi. Nau'ikan siffofi daban-daban sun haɗa da siffofin geometric, abstract, da kuma siffofin halitta, duk waɗannan mahimman abubuwa ne da suke samar da design.
🔰 Color
Launi wani bangare ne wanda yake da mahimmanci musamman wajen jawo hankali saboda akwai ilimin halayyar mutum a tattare da launi wanda zai iya haifar da sha'awa ko akasin hakan.
🔰 Typography
Rubutu ne na fasaha wanda yake shirya nau'ikan rubutu acikin design. Akwai muhimmanci sosai wajen saninshi domin yana iya shafar design dinka ta hanyar isar da saƙonka da kake son isarwa.
Rubutu ne na fasaha wanda yake shirya nau'ikan rubutu acikin design. Akwai muhimmanci sosai wajen saninshi domin yana iya shafar design dinka ta hanyar isar da saƙonka da kake son isarwa.
🔰 Texture
Texture a cikin design yana nufin yadda jikin duk wani rubutu zai kasance, misali rubutu na iya zama mai taushi, mai santsi, mai sheki ko kuma mai ƙarshi, da dai sauransu. Texture wani abu ne da ake amfani dashi don jan hankali a cikin design, Ana iya ƙara shi zuwa wasu abubuwa kamar siffofi, launuka, ko kuma hotuna.
Texture a cikin design yana nufin yadda jikin duk wani rubutu zai kasance, misali rubutu na iya zama mai taushi, mai santsi, mai sheki ko kuma mai ƙarshi, da dai sauransu. Texture wani abu ne da ake amfani dashi don jan hankali a cikin design, Ana iya ƙara shi zuwa wasu abubuwa kamar siffofi, launuka, ko kuma hotuna.
🔰 Space
Sarari yana nufin yankunan design da aka bari fanko ma'ana inda babu komai. Waɗannan yankuna sun haɗa da kowane na nesa ko yankuna tsakanin zagaye, ko ƙasa ko kuma sama. Wasu designers da gangan suna sanya sarari (space) a cikin zane don ƙara girmamawa ga yankunan design din.
Sarari yana nufin yankunan design da aka bari fanko ma'ana inda babu komai. Waɗannan yankuna sun haɗa da kowane na nesa ko yankuna tsakanin zagaye, ko ƙasa ko kuma sama. Wasu designers da gangan suna sanya sarari (space) a cikin zane don ƙara girmamawa ga yankunan design din.
🔰 Size
Size shine yadda wani abu yake ƙarami ko babba a cikin design. A cikin design ana amfani da girman nuni ga mahimmancin wani abu, size yana jawo sha'awar gani a cikin amfani da bambancin girma ko ƙanƙanta.
Comments
Post a Comment