Graphic Design Lesson 2

ƙA'IDOJIN GRAPHIC DESIGN Ka'idodin graphic design suna ba da shawarar yadda mai design ya fi dacewa ya tsara sassa daban -daban na aikinshi, dan tabbatar da ababen aikinshi gabaɗaya sun haɗu da juna cikin tsari. Manyan ƙa'idojin graphic design wadanda idan mutun ya kula dasu aikinshi yake yin kyau, idan kuma mutun yayi wofi dasu aikinshi yake lalacewa sune:- 🔰Balance 🔰Alignment BALANACE Samun daidaito na gani wato (balance) a cikin graphic design ya zama dole kuma wajiba ga dukkan wani graphic designer daya samar dashi madamar yana so saƙonshi ya isa cikin natsuwa ba tare da ru'dani ba. Ana samun wannan ta hanyar daidaita design a cikin nauyi - ana rarraba sifofi, layuka, da sauran abubuwa daidai. Don haka koda bangarorin biyu na design ba daidai suke ba, suna da abubuwa iri ɗaya. Daidaitawa yana da mahimmanci saboda yana ba da tsari da kwanciyar hankali ga design. Abubakar Ibrahim: ALIGNMENT Daidaitawa shine game da tsara design. Duk bangarorin design yakamata...