Computer Fundamental Darasi Na 5
Topic: Gyara da kanikancin kwamfuta. Wato duba da wannan lokaci da muke ciki a yanzu, an samu wayewar Kai sosai especially a harkar na’ura mai kwakwalwa. Kamar yadda kukasani a yanzu kowane ma’aikaci na office ko asibiti, ko gona ko magidanci ne ko dalibi ne, ko dan kasuwa, kowanne daga cikinsu kokarinsa ya iya kwamfuta duba da cewa ita computer tana da sauri gurin gudanar da aiyuka a saukake. Hakan yasa masu amfani da ita suka yawaita.. Kamar yadda nake fada dai ita computer abuce mai bukatar kulawa akai-akai, wasu zakaga duk bayan lokaci zuwa lokaci sukan kai na’urorin su gurin maintainance kamar ma’aikatan Banki da makamantansu. Shi wannan maintainance din bakomai bane illa duba lafiyar computer ko na hardware ko na software domin gujewa matsaloli irin nata... Hanyoyin da zakabi domin warware matsalolin kwamfutar ka.. Duk lokacin da ka lura da kwamfuta dinka ta samu matsala, idan har ba matsalar lalacewar wani component bane daga cikin kwamfutar ba, to tabbas ba buqatar k...